Ƙara daga darajar Naira ne yasa muke ƙara kuɗin ruwa – CBN

0 103

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce ƙarin kuɗin ruwa da aka dinga yi akai-akai ya taimaka wajen ƙarfafa gwiwar ‘yan ƙasar game da tunaninsu kan takardun kuɗi na naira.

Gwamnan CBN Olayemi Cardoso ya ce kuma bayyana matakin bankin na sake ƙara kuɗin ruwan zuwa kashi 27.25 a yau Talata jim kaɗan bayan kammala taron kwamatin harkokin kuɗi.

Hakan na nufin duk mutumin da ya ci bashin banki yanzu sai ya biya kuɗin ruwan kashi 27.25 na kuɗin da ya karɓa. CBN na cewa yana yin hakan ne da zimmar rage hauhawar farashi.

“Mun kusa faɗawa matsalar zagayawar kuɗi tsakanin jama’a a 2017 zuwa 2023, kuma mun ga yadda aka dinga zuba kuɗi a hannun jama’a,” in ji shi yana mai zargin wanda ya gada, Godwin Emefiele.

“A 2015, yawan kuɗin da ke zagayawa a hannun jama’a sun kai naira biliyan 19, a 2023 kuma tiriliyan 54. Wannan babban ƙari ne…Saboda haka buga takardun kuɗin na jawo yawan kuɗi.

“Saboda haka, mun yi imanin cewa yawan ƙara kuɗin ruwan ya taimaka wa mutane wajen sauya tunani game da takardun kuɗin, kuma yanzu akwai alfanu mai girma idan mutum yana riƙe da naira ba kamar a baya ba.”

A ƙarƙashin Cardoso – wanda ya fara aiki a watan Satumban 2023 – ana canzar da dala ɗaya kan naira 1,600, saɓanin N700 da ake canzarwa a lokacin da ya kama aikin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: