Ƙaramar hukumar Birniwa ta jihar Jigawa ta ƙaddamar da kwamitin bunƙasa harkokin ilmi mai wakilai 15

0 96

Karamar hukumar Birniwa ta kaddamar da kwamitin bunkasa harkokin ilmi mai wakilai 15.


Da yake kaddamar da kwamitin shugaban KH Alhaji Umar Baffa yace Karamar Hukumar ta kafa kwamitin ne bisa laakari da yadda iyayen yara ba sa yayansu a makaranta domin samun ilmin boko dana arabiyya.


Yace alhakin kwamitin ne ya zakulo yaran da suka isa shiga makaranta a kauyuka da rigagen yankin.


Alhaji Umar Baffa ya lura da cewar iyayen yara basa san sanya yayansu a makaranta yayinda aka cire wadanda suke karatun domin tura su zuwa almajiranci zuwa wasu wurare.


Wadanda aka kaddamar sun hadar da mataimakin shugaban KH Bello Wakili a matsayin shugaba yayinda Injiniya Adamu Galadima Diginsa zai kasance sakataren kwamitin

Leave a Reply

%d bloggers like this: