Ƙasar Masar ta fusata kan sanarwar da Habasha ta yi na cigaba da cike kogin Nilu

0 227

Ma’aikatar cikin gida a Masar ta ce maƙociya Habasha ta sabawa doka, kuma ba ta damu da yadda hakan zai shafi kasashensu ba.

Abiy Ahmed, firai ministan Habasha,ya sanar da ci gaban da aka samu a gina katafariyar madatsar ruwan da kasarsa ta gina da ta lakume dala biliyan 4 a jiya Lahadi.

Habasaha tace madatsar ruwan da aka kashe dalar amurca biliyan 4.2 bazata tare ruwan kogin na Nilu ba.

firai ministan Habasha Abiy Ahmed yace aikin ya gamu da tsaiko na cikin gida da waje, amma duk da haka sunyi nasara, madatasar ruwan ta fara samar da wutar lantarki tun a fabarerun 2022.

Madatsar ruwan dake samar da Mega Watt dubu 6 na lantarki tana da nisan kilo mita 30 da iyaka tsakanin kasashen Habasha da Sudan.

Tun shekarar 2011, kasashen Masar da Sudan suke takaddama da Habasha akan batun cike kogin na Nilu. Sai dai gwamnatin Habasha ta kafe da cewa madatsar ruwan ta na da muhimmanci wajen samar da wutar lantarki ga miliyoyin ‘yan kasar, da ta taka rawa wajen rage talauci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: