Ƙasar Rwanda ta karbi ‘yan gudun hijira 91 da masu neman mafaka daga kasar Libya

0 139

Ƙasar Rwanda ta karbi ‘yan gudun hijira 91 da masu neman mafaka daga kasar Libya a karkashin wani shiri da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, da kungiyar tarayyar Afrika da kuma Tarayyar Turai ke tallafawa.

Ƴan gudun hijirar sun haɗa da ‘yan Sudan 38 da ‘yan Eritriya 33 da ƴan Somaliya 11 da ƴan Habasha bakwai da kuma ‘yan Sudan ta Kudu biyu.

An kwashe ‘yan gudun hijirar da masu neman mafaka a karkashin shirin gaggawa na jigilar kayayyaki, wanda ya ga ‘yan gudun hijira 2,150 da aka aika zuwa Rwanda daga Libya tun daga shekarar 2019.

Daga cikin waɗannan, 1,600 sun yi ƙaura zuwa Amurka da ko’ina cikin Turai. Zuwan ‘yan gudun hijirar da masu neman mafaka ya zo ne a daidai lokacin da Birtaniya ke ƙokarin samar da sabuwar dokar da za ta ba ta damar tura wasu masu neman mafaka zuwa Rwanda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: