Ƙasar Sin ta ce za ta tura tawagar ƙwararru ta musamman kan binciken laifuka domin tattaunawa da hukumomin tsaron Najeriya

0 109

Ƙasar China ta ce za ta tura tawaga ta musamman ta ƙwararru kan binciken laifuka domin tattaunawa da hukumomin tsaron Najeriya.

Jakadan ƙasar China a Najeriya Cui Jianchun ne ya sanar da hakan a jiya, inda ya ce China za ta yi haka ne saboda ta damu kan matsalolin tsaron da Najeriyar ke fama da su.

Mista Cui ya bayyana cewa wannan yunƙurin da China ke yi na daga cikin goyon bayan da take ba ƙasar wajen magance matsalolin tsaro inda ya ce nan ba da jimawa ba ƙwararrun za su isa Najeriyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: