Ƙasashen Sifaniya da Norway da kuma Ireland zasu kulla alaka da ƙasar Falasɗin

0 202

Ƙasashen Sifaniya da Norway da kuma Ireland na shirin kulla alakar da ƙasar Falasɗin cikin mako mai zuwa.

Ƙasashen uku sun bayyana ranar 28 ga watan Mayun da muke ciki a matsayin ranar da zasu aiwatar matakin.

Firaministan Madrid, Pedro Sanchez, ya ce firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu yayi kunnen ƙashi, inda yake ci gaba da kai hare-haren boma-bomai kan asibitoci da makarantu tare da azabtar da mata da ƙananan yara da yunwa da kuma tsananin sanyi.

A nasa ɓangare firaministan Ireland, ya ce ”samun yancin ƙasashen biyu shi ne kawai mafita a ƙoƙarin samar da zaman lafiya”.

A farkon wannan watan ƙasashe 143 daga cikin ƙasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya 193, sun kaɗa ƙuri’ar amincewa da Falasɗinu ta shiga cikin MDD, wani abu da ƙasa mai zaman kanta ne kawai ke samun damar haka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: