Ƙungiyar Ƙwadago za ta yi zaman gaggawa kan karin farashin man fetur

0 97

Ƙungiyar Ƙwadago ta kasa, NLC, ta bayyana shirinta na zaman gaggawa dangane da karin kashi 45 cikin 100 a farashin man fetur da Kamfanin Man Fetur na kasa, NNPCL, ya yi kwanan nan.

Wannan na zuwa ne yayin da ƙungiyar ta buƙaci Kamfanin Man Fetur na (NNPCL) da ya janye ƙarin farashin da ya kai Naira 855 zuwa Naira 897 da ya yi a jiya Talata.

Ƙungiyar Ƙwadagon ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Comr Joe Ajaero, ya sanya wa hannu a jiya Talata, a matsayin martani ga ƙarin farashin fetur ɗin.

Ƙungiyar NLC ta kara da cewa gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta ci amanar ta.
Haka kuma, ƙungiyar ta bukaci a saki duk masu zanga-zangar da ake tsare da su, sannan kuma ta nemi a janye ƙarin farashin wutar lantarki da aka yi a watan Afrilu na 2024 da ya kai kashi 250 cikin 100.

Leave a Reply

%d bloggers like this: