Ƙungiyar ƴan adaidaita sahu a jihar Kano ta buƙaci mambobinta da su koma bakin aikin su daga yau

0 177

Ƙungiyar ƴan adaidaita sahu a jihar Kano ta buƙaci mambobinta da su koma bakin aikin su daga yanzu.

Shugaban ƙungiyar a jihar Kano Alhaji Sani Sa’idu Ɗan Koli ne ya tabbatar da hakan ga Freedom Radio da yammacin ranar Talata.

Ɗan koli ya ce “Bayan umarnin majalisar dokokin jihar Kano yanzu haka mun kammala ganawa da hukumar DSS wadda ta bamu tabbacin janye yajin aiki”.

“DSS ta sanar da mu cewa gobe Laraba da ƙarfe 10 na safe za mu ji kyakkyawan labari don haka daga yanzu kowanne mai adaidaita sahu zai iya fita domin ci gaba da kasuwancinsa”.

Ɗan Koli ya kuma ce, yana mai bai wa direbobin babura masu ƙafa uku tabbacin cewa matsalolin su sun zo ƙarshe.

Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaban majalisar dokokin jihar Kano Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ya buƙaci ƙungiyar ƴan adaidaita sahun da su janye yakin aikin da suke domin kuwa za su shiga tsakani don sulhuntawa.

Freedom Radio

Leave a Reply

%d bloggers like this: