Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya ta kai ziyarar jaje ga gwamnan jihar Sokoto bisa kisan wasu yan asalin jihar da ƴanta’adda suka yi

0 251

Kungiyar Gwamnonin kasar nan ta kai ziyarar jaje ga alumma da kuma Gwamnan jihar Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal bisa kisan wasu yan asalin jihar da yan taadda suka yi.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Ekiti Dr Kayode Fayemi wanda ya jagoranci tawagar yace sun je Sokoto ne domin jajanta wa jama’a da Gwamna da iyalan wadanda abin ya shafa.

Ya bayyana alamurran a matsayin abin tausayawa inda ya bada tabbacin kungiyar na cigaba da kare muradin alummar kasar nan.

A jawabinsa Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya jajanta wa mutane 42 da ‘yan bindiga suka kashe tare da yin addu’a ga wadanda abin ya shafa.

Ya kuma nemi jama’a dasu cigaba da yin adduoi domin kara samun kariya daga abubuwan dake faruwa a kasar nan inda yace shugaban kasa Muhammadu Buhari na yin duk mai yiwuwa domin kare dukiyoyin da rayukan alummar kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: