

- Mataimakin Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi, shine ya lashe zaben fidda gwani na dan takarar gwamna a jam’iyyar APC - May 27, 2022
- Shugaba Buhari yace gwamnatinsa tana assasa ginshiki mai inganci na kyakykyawar rayuwa domin yara manyan gobe a Najeriya - May 27, 2022
- Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta haramta bangar siyasa da tare da yin amfani da duk wani makami ga yaran yan siyasa - May 27, 2022
Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ta Academic Staff Union of Universities (ASUU) ta ayyana shiga yajin aiki na sati huɗu a matsayin gargaɗi ga gwamnatin tarayyar ƙasar.
Shugaban ASUU Farfesa Emmanuel Victor Osodeke ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a yau Litinin bayan wata ganawa da majalisar zartarwar ƙungiyar ta yi ta tsawon kwana biyu.
Shugaban ƙungiyar reshen Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil, Kano ya ce shugabannin ƙungiyar na jihohoi na kan hanyarsu ta komawa don sanar da ƙungiyoyin nasu halin da ake ciki.
Tun a ranar Asabar ne shugabannin ASUU suka fara ganawa a Jami’ar Legas (UNILAG) don cimma matsaya kan abin da suka kira “saɓa alƙawari na gwamnatin tarayya” ƙarƙashin Shugaba Muhammadu Buhari.
Malaman jami’ar da suka dakatar da aiki tsawon wata tara a 2020, sun sha kokawa kan halin da ilimi ke ciki a Najeriya, ciki har da maganar albashinsu.
BBCHausa