Ƙungiyar NLC tana tattara bayanan jihohin da har yanzu ba su fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ba

0 109

Ƙungiyar Ƙwadago ta kasa, NLC, ta ce tana tattara bayanan jihohin da har yanzu ba su fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na naira dubu saba’in ba ga ma’aikata. 

Mataimakin shugaban ƙasa na ƙungiyar, Kwamared Ado Minjibir, ne ya bayyana haka a cikin wata hira da aka yi da shi a shirin Bakonmu na Radio Jigawa. 

Ya ce ƙungiyar na raba jihohin kashi uku, waɗanda suka amince da biyan sabon albashin amma ba su fara ba, da waɗanda ke biyan ƙasa da abin da doka ta tanada, da kuma waɗanda suka cika sharudan sabuwar tsarin biyan albashi. 

Kwamared Ado ya ƙara da cewa ƙungiyar na bibiyar lamarin domin ɗaukar matakin doka a inda ya dace, tare da bayyana cewa an rage tazara tsakanin sabunta albashi daga shekara biyar zuwa shekara uku kamar yadda doka ta tanada.

Leave a Reply