A Jamhuriyar Nijar ,gamayar Ƙungiyoyin Ƙwadago na malaman makarantun boko da na koyar da sana’a da fasahohi ne suka tsunduma wani yayin aikin gargaɗi na kwanaki uku, domin nuna fushinsu game da yanda gwamnati ta yi watsi da wasu jerin buƙatunsu musamman dauƙar yan kwantragi aikin na din din.
Wannan yajin aikin shine mafi girma da wata ƙungiya ta shiga tun bayan da sojoji suka karɓi mulki a kasar da ke yammacin Afirka.
Ture bukatar ɗaukar ‘yan kwantaragi aikin din din, da gaza biyan wasu alawus ne suka harzuka gamayar Ƙungiyoyin malaman makarantu shiga yajin aiki, don su nuna matsayinsu.
Tuni dai malaman makarantu suka yi maraba da wannan kira na yajin aikin, inda suka kaurace wa makarantun.
Yajin aikin ya zo a lokacin da ake ta shirye shiryen fara rubuta jarabawar ƙarshen zangon shekara, abin da ya sanya ma iyaye ke ganin wannan yajin aiki ‘yayansu zai shafa ba wai gwamnati ba.
Ganin yanda yajin aikin ya dakatar da harakar ilimi ya sa gwamnati ta Kira wani taron don tantamnawa da kungiyoyin a gobe lamarin da wasu kungiyar yan kwantragi ta ce ba da ita ba gada a kabari.
Rarbawa :