Kungiyyar kiristoci ta kasa CAN ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo karshen kisan kiristoci da yan ta’adda sukeyi a jihar Zamfara ko kuma su dauki matakin kare kansu.

Kungiyyar ta kuma bukaci hukumomin tsaro da su bawa wuraren ibadar su kariya damon dakile dukwata irin barazana da kiristoci zasu fuskanta a fadin kasar nan.

Sakataren kungiyyar na kasa Joseph Bade Daramola ne ya bayyana hakan, yayin dayake maida martani akan takardar barazana da aka aikewa mabiya addinin a jihar Zamfara, akan su rife wuraren idaba, ko kuma su fuskanci hare hare daga yan bindiga.

Cikin takardar da Ademola ya fitar, ya bayyana cewa tinda yanzu babbar kotin tarayya ta ayyana yan bindiga a matsayin yan ta’adda, to dole yansanda da soji su dauki matakin magance su, musamman a yankunan da Garkuwa da mutane ya zama ruwan dare.

Ya kara da cewa hanyar da jami’an tsaro suke bi a halin yanzu wajan yaki da ta’addaci abin a sake nazarta ne, kuma idan aka tafi a haka bazata haifar da Da mai ido ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: