Ƴan bindiga sun kashe jami’an tsaro 7 a Zamfara

0 110

Sojoji uku da ƴan sanda huɗu ne suka mutu a wani harin kwantar ɓauna da ƴan bindiga suka kai musu a lokacin da suke ƙoƙarin tarwatsa ƴan bindigan da suka kai wani hari a Zamfara a ranar Alhamis.

Kwamishinan ƴansanda jihar, Mohammed Dalilan ne ya bayyana hakan, inda ya ce ƴan bindigan sun shirya kai wani hari a wani kamfanin gine-gine da suke aikin titi a jihar.

Ya ce hakan ya sa haɗakar sojoji da ƴansanda suka kai ɗauki, inda aka yi rashin sa’a, ƴan bindigan suka musu kwantar ɓauna, suka buɗe musu wuta.

Kwamishinan ƴansanda ya bayyana cewa jami’an tsaron sun yi ƙoƙarin gaske wajen dakatar da harin.

“Sun yi niyyar zuwa kamfanin Setraco ne domin garkuwa da ma’aikatan kamfanin, da muka samu labari, sai muka tura dakarunmu, ashe sun ɗana musu tarko, inda suka yi kwantar ɓauna suka buɗe musu wuta,” inji shi kamar yadda shafin talabaijin na Channels na intanet ya ruwaito.

Ya ƙara da cewa dakarun sun mayar da martani, inda bayan musayar wuta, sojojin suka samu nasarar dakatar da harin, “amma mun rasa sojoji uku da ƴansanda huɗu.”

Leave a Reply

%d bloggers like this: