Ƴan bindiga dauke da makamai sun kai mummunan hari a ƙauyen Marmara da ke ƙaramar hukumar Malumfashi a jihar Katsina. Maharan sun kashe dakarun tsaro huɗu na rundunar Community Watch Corps (CWC) da kuma tulin manoma da ba a tantance adadinsu ba zuwa yanzu.
Wani mai magana kan harkokin tsaro, Bakatsine, shi ne ya wallafa abin da ya faru a shafinsa na manhajar X ranar Talata.Harin wanda ya auku da yammacin Litinin, ya faru ne a wajen gari, inda wasu manoma ke aiki a gonakinsu, kafin ‘yan bindigar su kawo farmakin ba zato ba tsammani. Bakatsine ya rubuta a shafinsa cewa: “Da Yammacin jiya, ƴan bindiga sun farmaki manoma a wajen garin Marmara, karamar hukumar Malumfashi a jihar Katsina. “An kashe jami’an CWC guda hudu da suka yi ƙoƙarin daƙile harin, an kuma kashe wasu manoma da dama, yayin da wasu kuma suka jikkata.
Rahoton Leadership ya nuna cewa Gwamnatin Katsina ta fara ƙoƙarin sasantawa da ƙungiyoyin ‘yan bindiga a wasu sassan jihar domin dawo da zaman lafiya. A cewar rahoton, wasu daga cikin ƴan bindiga a Jibia, Batsari, da DanMusa sun amince da yarjejeniyar zaman lafiya kuma sun mika makamansu. Sai dai wannan sabon hari a Marmara ya haifar da fargaba da shakku a zukatan mazauna yankin, game da inganci da dorewar irin wannan yarjejeniya da ‘yan bindigar.
Wani mazaunin yankin ya bayyana damuwarsa da cewa: “Mun fara ganin alamar zaman lafiya, amma wannan hari ya komar da mu baya. Idan har za a ci gaba da kisan bayin Allah duk da shirin sulhu, to akwai buƙatar a sake duba tsarin.” Har kawo yanzu rundunar ƴan sanda ko gwamnatin jihar Katsina ba su fitar da wata sanarwa dangane da harin ba, amma jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike a yankin.
Ana sa ran gwamnati da hukumomin tsaro za su dauki matakin gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, musamman yayin da damina ta karato kuma manoma ke komawa gona.