Ƴan bindiga sun sake kashe biyu daga cikin ɗaliban jami’ar Greenfield a Kaduna

0 234

Ƴan bindiga da suka sace ɗaliban jami’ar Greenfield a Kaduna arewacin Najeriya sun sake kashe biyu daga cikin ɗaliban.

Cikin sanarwar da kwamishinan lamurran tsaro Samuel Aruwan ya fitar ya ce an tsinci gawar ɗaliban ne a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce “Gwamnatin Malam Nasir El-Rufai tana bakin cikin wannan mummunar aiki da aka yi wa ɗaliban da ba su ji ba ba su gani ba da aka sace yayin da suke ci gaba da neman iliminsu don samun makoma mai kyau.”

A makon da ya gabata ƴan bindigar suka kashe uku daga cikin ɗaliban waɗanda ƴan bindiga suka sace a ranar Tatalar da ta gabata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: