Wasu yanmata 4 sun nutse a kogi sun mutu a kauyen Kafin Doki Yamma dake yankin karamar hukumar Gwaram a nan jihar Jigawa.

Kakakin rundunar yan sandar jihar jigawa SP Abdu Jinjiri ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Dutse.

A cewarsa lamarin ya faru ne a safiyar jiya talata a lokacin da yaran suke kokarin tsallake kogin domin zuwa gona.

Ya kara da cewa yanmatan hudu da suka mutu sun hada Bilkisu Haruna mai shekara 17, Shamsiyya Nuhu yar shekara 13, da Maryam Danlami shekara 12 da kuma  Marakisiyya Musa mai shekara 13 a duniya, dukkanin su yan asalin kauyen Kafin Doki ne dake mazabar Sara a karkashin karamar hukumar Gwaram.

Abdu Jinjiri ya kara da cewa ansamu nasarar tsamo gawar uku daga cikin su, sannan ana ci gaba da neman daya gawar.

Kazalika ya kara da cewa likita ya tabbatar da mutuwar wadanda akayi nasarar samun gawar ta su.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: