Ƴansanda sun ceto barawon babur daga hannun fusatattun matasa a garin Kazaure

0 74

‘Yansandan a jihar Jigawa sun ceto wani da ake zargin barawon babur ne daga hannun wasu fusatattun matasa a karamar hukumar Kazaure.

Wani mazaunin garin ya shaidawa manema labarai cewa lamarin ya faru ne a unguwar Shaiskawa a jiya Talata.

Ya ce mutanen yankin sun kafa wa barawon tarko ne saboda yawaitar satar da ake yi a yankin kuma sun yi nasarar cafke wanda ake zargin a lokacin da ya yi yunkurin satar babur.

A cewarsa, “A dalilin haka ne matasan da suka fusata suka yi masa dukan tsiya ba tare da tausayi ba, kuma ‘yan sanda sun ceto shi.”

Kakakin rundunar, DSP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.
Ya ce da ake yi masa tambayoyi wanda ake zargin ya amsa laifinsa, ya bayyana cewa ya isa garin Kazaure ne a ranar kasuwa da niyyar satar babur.

Leave a Reply

%d bloggers like this: