Ƴansanda sun haramta zanga-zanga a ƙwaryar babban birnin kasar Kenya

0 104

Ƴansanda a kasar Kenya sun haramta zanga-zanga a ƙwaryar birnin kasar Nairobi da kewaye har sai abin da hali ya yi la’akari da rashin jagoranci da rundunar ‘yansandan ƙasar ke fuskanta bayan ajiye aiki da shugabanta ya yi, lamarin da rundunar ta ce na kawo mata tarnaƙi a aikinta.

Haramcin na zuwa ne wata guda bayan zanga-zangar nuna adawa da wasu manufofin gwamnati, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar gomman masu zanga-zangar.

An shirya ƙaddamar da wata zanga-zangar a yau Alhamis a wajen shaƙatawa na Uhuru da ke tsakiyar birnin Nairobi, inda daga nan ne za su yi tattaki zuwa gigan gwamnati da shugaban ƙasar ke zama.

Nairobi ta kasance cibiyar zanga-zangar da matasan ƙasar ke yi wadda ta bazu zuwa sauran sassan ƙasar.

Zanga-zangar ta fara ne kan ƙin amincewa da ƙarin haraji da gwamnatin ƙasar ke son yi.

A yanzu haka an ajiye jami’an tsaro masu yawa a sassan birnin gabanin zanga-zangar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: