Ƴansanda sun kashe ƙasurgumin ɗanbindiga Dogo Saleh

Rundunar ƴansandan birnin Tarayya Abuja ta sanar da kashe wani ƙasurgumin ɗanbindiga mai garkuwa da mutane, Dogo Saleh da ya birnin.
Kakakin rundunar ƴansandan birnin, SP Josephine Adeh ta shaida wa BBC cewa ɗanbindigar tare da yaransa sun addabi wasu sassan birnin Abuja, inda suke ayyukan garkuwa da mutane.
Ta ƙara da cewa sakamakon bayanan sirri da suka samu kan maɓoyar ɗanbindigar ya sa suka tura jami’ai maɓoyar domin kama shi.
”Sai dai sakamakon gumurzun harbe-harbe da jami’anmu, mun samu nasarar kashe ɗanbindigar da wasu yaransa ”, in ji kakakin ƴansandan birnin.
Ta kara da cewa ɗanbindigar – wanda shi ne babban mataimakin shugaban ƴanbidigar – ya yi ƙaurin suna wajen ayyukan ta’addanci a kan titin Abuja zuwa Kaduna.
SP Adeh ta ce a lokacin gumurzun jami’an ƴansanda sun kuɓutar da wasu mutane da ɗanbindigar ke garkuwa da su.