Ƴansanda sun kuɓutar da mutum 73 da aka yi garkuwa da su a Katsina

0 140

Rundunar ƴansandan jihar Katsina ta ce ta ceto mutum 73 da aka yi garkuwa da su.

Ta kuma ce ta kama mutum 75 waɗanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban a faɗin jihar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴansandan jihar, Abubakar Sadiq ya fitar, ta ce ana zargin mutum 15 cikin mutanen da laifin fashi da makamai, yayin da wasu 20 kuma da laifin kisa.

“An kama mutum guda da laifin mallakar bindiga, 30 da zargin aikata fyaɗe sannan 108 kuma an kama su ne da wasu laifukan,” in ji sanarwar.

Sadiq ya ce makaman da aka ƙwato daga wajen mutanen sun haɗa da bindigar AK-49, karamar bindiga ƙirar pistol, ɗaruruwan harsasai, babura biyu da kuma shanu 174 da ake zargin sun sace.

Ya ce ana ci gaba da kula da waɗanda aka kuɓutar daga hannun masu garkuwan.

Leave a Reply