Ɓallewar dam a Kudancin Sudan a ranar 24 ga Agusta bayan mamakon ruwan sama ya kashe sama da mutum 60, kamar yadda jaridar Akhbar ta intaneta mai zaman kanta a Sudan ta ruwaito.
Kafar ta ruwaito cewa bayan bakin tekun ya ɓalle a ƙauyen Arbaat, kilomita 20 daga Port Sudan, ambaliyar ruwa zai iya ƙaruwa. Dam ɗin ne ke ba mutanen yankin ruwa.
Rundunar sojin Sudan da sauran jami’an tsaro sun shiga cikin ayyukan ceto, domin ceto mutanen da suka maƙale.
Haka kuma ambaliyar ta ɗaiɗaita “ƙauyuka 15” kamar yadda rahoton ya nuna.
A wani ɓangaren kuma, jaridar Tribune mai zaman kanta a ƙasar ta ruwaito cewa a sanadiyar malalewar ruwan dam ɗin, za a iya shiga matsalar ƙarancin ruwa a yankin na Port Sudan, inda a nan shugabannin sojin suke gudanar da mulki a daidai lokacin da ƙasar ke tsaka da yaƙi da Rundunar RSF, wanda aka fara tun a Afrilun 2023.
Sama da mutum 100 ne suka mutu, sannan ɗaruruwa sun samu rauni a ambaliya da ta dabaibaye ƙasar ta Sudan a ƴan makonnin da ake ciki.