Ɗaliban gaba da makarantar sikandire suna zanga-zanga kan yajin aikin ASUU a Kano

0 264

Dalibai a Kano

Ɗalibai a Najeriya sun fito zanga-zanga a Kano domin nuna rashin jnn daɗinsu kan yajin aikin da ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU.

Sun fara tattakin ne daga karkashin kofar Nasarawa, sannan suka shiga gidan Murtala don isar da sakonsu ga Kwamishinayar da ke kula da manyan makarantu.

Zanga-zangar Dalibai

An samar da jami’an tsaro na DSS da ƴan Sanda daga ƙofar Nasarawa zuwa dukkan mahaɗa ta zuwa gidan gwamnatin Kano, da karkashin gadar Nasarawa.

Tun a makon jiya ƙungiyar ɗaliban ta ƙasa NANS ta ce za ta ƙaddamar da zanga-zanga a manyan biranen Najeriya kan yajin aikin ASUU.

Leave a Reply

%d bloggers like this: