Ɗan majalisar wakilan Najeriya daga Neja ya yi ƙaura daga jam’iyyar PDP mai adawa zuwa APC mai mulki
Ɗan majalisar wakilan Najeriya daga jihar Neja, Hon. Adamu Lokoja, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Adamu Lokoja yana wakiltar mazaɓar Suleja, Gurara da Tafa a majalisar wakilan Najeriya.
Shugaban APC na jihar Neja, Alhaji Aminu Bobi, ne ya karɓe shi a hukumance cikin jam’iyyar APC a hedkwatar jam’iyyar da ke Minna, babban birnin jihar Neja, cewar rahoton tashar Channels tv.
Yayin taron tarba da aka gudanar cikin girmamawa, shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Neja ta Gabas, Danladi Ahijoh, na daga cikin waɗanda suka yi bayani.
Ya bayyana cewa sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC tamkar saka jari ne ga duk wani ɗan siyasa da ke da buri da sha’awar kasancewa cikin waɗanda za a riƙa damawa da su a nan gaba.
A cewarsa, dalilan da suka jawo sauya sheƙar Hon. Adamu Lokoja sun haɗa da manufofin ci gaba da sauya fasalin mulki da ake gani a ƙarƙashin jagorancin jam’iyyar APC.