Ƙungiyar cigaban al’ummar Gobirawa ta rubuta wa shugaba Buhari wata buɗaɗɗiyar wasika saboda taɓarɓarewar tsaro a Arewa

0 202

Kungiyar ci gaban al’ummar Gobirawa ta Kasa reshen Karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto ta rubuta wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wata budaddiyar wasika wadda take neman ya kawo karshen kashe-kashen da ake yi a arewacin kasar nan.

Kiraye-kirayen na zuwa ne a daidai lokacin da bai wuce Awanni 24 ba, wasu yan bindiga suka kone wasu Matafiya a kyauyen Gidan Bawa a karamar hukumar ta Sabon Birni.

Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, ya ce kimanin mutane 23 ne Jami’an tsaro suka tabbatar da mutuwar su.

Wasikar ta zayyano dimbin matsalolin da yankin ke fama da su da kuma wasu hanyoyi da suke ganin idan an bi, za a iya magance wadannan matsaloli.

Budaddiyar wasikar ta nuna damuwa kan kashe-kashen mutanen da ake yi ba tare da daukar mataki ba – musamman a kananan hukumomin Sabon Birni da Goronyo da Isa da kuma Shinkafi da ke jihohin Sokoto da Zamfara.

Sanarwar ta ce a kwanakin baya kimanin Mutane 80 ne yan bindigar suka kashe a kyauyen Garki dake Karamar Hukumar Sabon Birni cikin dare guda.

Kazalika, mutanen sunyi Alkawarin tallafawa Jami’an tsaro wajen ganin cewa sun kai ga Nasara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: