Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta African Union ta dakatar da Sudan daga cikinta har sai an dawo da mulkin farar hula a ƙasar

0 183

Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta African Union ta dakatar da Sudan daga cikinta har sai an dawo da mulkin farar hula a ƙasar.

Ta ce juyin mulkin da sojoji suka yi ranar Litinin ya saɓa wa kundin tsarin mulki.

Zanga-zangar nuna ƙin jinin juyin mulkin na ci gaba a birnin Khartoum rana ta uku a jere.

Ƙungiyar ma’aikatann kamfanin man fetur ta Sudapet za ta shiga zanga-zanga, yayin da ƙungiyar likitoci za ta fara yajin aiki na game-gari.

Tun farko Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya yi magana da Firaminista Abdalla Hamdok, wanda aka tumɓuke, bayan ya koma gida daga hannun sojojin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: