Ƴan sandan Chadisun tarwatsa masu zanga-zanga da hayaƙi mai sa ƙwalla

0 198

Ƴan sandan Chadisun tarwatsa masu zanga-zanga da hayaƙi mai sa ƙwalla a Ndjamena babban birnin ƙasar, inda daruruwan mutane suka fito suna adawa da shugabannin soji.

Magoya bayan ‘yan adawa sun ce mutane da dama sun jikkata.

Ƴan sanda sun ce sun yi harbi ne kan masu zanga -zangar saboda sun ƙetara iyaka, ba su tsaya kan hanyar da aka ba su izinin yin zanga-zangar ba.

Sojojin sun karɓe iko ne a watan Afrilun bana bayan mutuwar shugaba Idriss Deby.

An naɗa ɗansa, Janar Mahamat Deby, a matsayin shugaban ƙasa.

A kwanan ne sabon shugaban ya ce za a iya tsawaita wa’adin da aka ɗiba na miƙa mulki watanni goma sha takwas idan ba a cika wasu sharuɗɗa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: