Labarai

Yan bindiga dauke da makamai sun kashe mutum 7 yan’uwan juna a kauyen Sabon Birni na jihar Kaduna

Yan bindiga dauke da makamai a jiya sun kashe wasu mutane 7 ‘yan’uwan juna a wani hari a kauyen Sabon Birni a yankin karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna. Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai yau da safe. Samuel Continue reading
Labarai

ASUU bata da dalilin tafiya yajin aiki saboda mun biya – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya tace kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) bata da dalilin tafiya yajin aiki kasancewar ta biya dukkan bukatusn malaman dai-dai nauyin aljihunta. Daraktan yada labarai da huldar jama’a na ma’aikatar ilimi ta tarayya, Ben Bem Goong, ya zanta da manema labarai lokacin da yake Continue reading
Labarai

‘Har yanzu gwamnatin Najeriya bata ayyana ‘yan fashin daji a matsayin ‘yan ta’adda ba’ – Malami

Babban lauyan tarayya kuma ministan shari’ah, Abubakar Malami, yace har yanzu gwamnatin tarayya bata ayyana ‘yan fashin daji a matsayin ‘yan ta’adda ba, saboda gwamnati tana koyi da sauran manyan kasashen duniya. Yace ofishinsa yana kan aikin fara aiwatar da umarnin kotu da ya umarci gwamnati Continue reading
Labarai

Masu fafutukar kare mulkin demokradiyya a kasar Sudan zasu cigaba da sabbin zanga-zanga

Masu fafutukar kare mulkin demokradiyya a kasar Sudan sun sanar da sabbin zanga-zanga daidai lokacin da rikicin siyasa ya kara muni bayan murabus din Fira-Ministan Abdalla Hamdok a jiya. Akalla masu zanga-zanga 3 aka kashe a ranar Lahadi bayan dubban masu zanga-zangar dake adawa da mulkin Continue reading
Labarai

Akalla mutane 4 ne suka mutu a wani hadarin mota tsakanin wasu motocin haya guda 3 a jihar Sokoto

Akalla mutane 4 ne suka mutu a wani hadarin mota tsakanin wasu motocin haya guda 3 a jihar Sokoto. Hakan ya haifar da zanga-zanga daga wasu fusatattun matasa wadanda suka cinna wuta kan wasu motaci biyu na hukumar hana fasa kwauri ta kasa (custom). Fusatattun matasan sun dora alhakin hadarin da Continue reading
Labarai

Sama da mutum 50 da gawurtaccen dan fashin daji Bello Turji ya sace sun shaki iskar ‘yanci

Sama da mutane 50 da gawurtaccen dan fashin daji Bello Turji ya sace, sun shaki iskar ‘yanci. Shugaban kwamitin kawo karshen fashin daji na jihar, Dr. Abdullahi Shinkafi, ya tabbatar da hakan ga manema labarai yau da safe. Dr. Shinkafi yayi nuni da cewa wadanda aka sace sun kai 70, inda ya kara Continue reading
Labarai

Kungiyar RIFAN zata gudanar da bikin shinkafa da nufin tallafawa yunkurin gwamnatin tarayya na wadatar da abinci a Najeriya

Kungiyar manoman shinkafa ta kasa (RIFAN) na shirin gudanar da bikin shinkafa a Abuja da nufin tallafawa yunkurin gwamnatin tarayya na wadatar da abinci a kasarnan. Ana sa ran za a gudanar da bikin a harabar cibiyar kasuwanci da masana’antu ta Abuja, kuma tuni aka yi nisa a shirye-shiryen samun Continue reading
Labarai

Kwamitin Zakka ta masarautar Kazaure ta raba kayan abinci da kudinsu fiye da naira miliyan 17

Kwamitin Zakka na masarautar Kazaure yace ya raba kayan abinci da kudinsu ya kai naira miliyan 17 da dubu 671 da 500 ga mabukata dubu 3 da 646 a gundumomin Amaryawa da Dandi dake masarautar a wani bangare na kokarin rage yunwa tsakanin marasa galihu. Shugaban kwamitin, Bala Muhammad Kazaure, ya Continue reading
Labarai

Ministan wutar lantarki yace za a iya samun karuwar wutar lantarkin kasarnan fiye da megawatt dubu 5

Ministan wutar lantarki, Engineer Abubakar Aliyu, yace za a iya samun karuwar wutar lantarkin kasarnan fiye da megawatt dubu 5 da za ake watsawa da rarrabawa idan aka aiwatar da ayyukan wutar lantarki da aka bayar na kudi naira miliyan dubu 43 da miliyan 750. Wata sanarwa daga kakakinsa, Isa Continue reading
Labarai

Gwamna Badaru ya wakilci shugaban kasa Buhari a wajen bikin rufe taron tarihi na wasan gargajiya na kasar Nijar

Gwamnan Jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari a wajen bikin rufe taron tarihi na wasan gargajiya na kasar Nijar karo na 42 da aka gudanar a birnin Yamai babban birnin kasar. Gwamnan wanda ya jagoranci tawagar shugaban kasa ya samu tarba daga shugaban Continue reading