Labarai

Hukumar NCDC tace mutum 48 sun sake kamuwa da zazzabin Lassa

Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta ce an samu rahotan bullar zazzabin Lassa guda 48 cikin wannan shekarar ta 2022. Rahotan da Cibiyar ta fitar ya yi nuni da cewa an samu rahotan bullar cutar ne daga ranar 3 zuwa 9 ga watan Janeru da muke ciki. Hukumar ta NCDC ta ce an […]Continue reading
Labarai

Gwamnonin jam’iyyar PDP suna gudanar da taron ganawar sirri

Gwamnoni 12 na Jam’iyar PDP ciki harda Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara Barista Mahdi Aliyu, suna gudanar da taron ganawar sirri a Gidan Gwamnatin Jihar Rivers da ke birnin Fatakol. Kimanin Gwamnoni 13 ne suka halarci zaman sai dai kuma Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki, bai halarci zaman ba, Continue reading
Labarai

‘Karancin malamai a Makarantun Polytechnics na cigaba da dakushe kokarin kwalejojin wajen samar da Ilimi mai inganci’

Hukumar Lura da Ilimin Kwalegin Fasaha ta Kasa ta ce Karancin Malamai a Makarantun Polytechnics na cigaba da Dakushe kokarin Kwalejojin wajen samar da Ilimin Fasaha a kasar nan. Hukumar ta ce Kwalejojin Fasaha Mallakin Gwamnatin tarayya na fuskantar mutuwa, biyo bayan karancin Malamai, kuma Continue reading
Labarai

Kungiyar Gwamnonin jam’iyar APC sun nanata cewa za su gudanar da babban taron kasa a watan Fabreru

Kungiyar Gwamnonin da aka zaba karkashin tutar Jam’iyar APC sun sake nanata cewa Jam’iyar zata gudanar da babban taron ta na Kasa a watan Fabreru na wannan shekara. A watan Nuwambar shekarar bara ne, Shugaban Kungiyar kuma Gwamnan Jihar Kebbi Atiku Bagudu, da Gwamna Badaru Abubakar sun bayyana Continue reading
Labarai

Angudanar da ayyukan noma na fiye Naira miliyan 17,000 a kananan hukumomin 5 na jihar Jigawa

Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwiwar bankin cigaban Afrika sun gudanar da ayyukan noma da kudinsu ya kai naira miliyan dubu 17 da miliyan 700 a kananan hukumomin 5 na jihar Jigawa. Sanata mai wakiltar Jigawa ta arewa maso gabas Barista Ibrahim Hassan Hadejia ya sanar da hakan a lokacin duba Continue reading
Labarai

Shugaban jami’ar Khadija dake Majia ta rage kaso 50 ga yan asalin jihar Jigawa

Gidauniyar Mallam Adamu Majiya Memorial Foundation ta amince da rangwamen kashi 50 cikin 100 na kudin shiga jamiar Khadija dake Majia ga yan asalin jihar Jigawa da suka cancanta domin yin karatun digiri a shekarar karatu ta 2021 zuwa 2022. Haka kuma gidauniyar ta yi rangwaman kashi 30 cikin na Continue reading
Labarai

Ma’aikatar ilimi ta jihar Zamfara ta sanar da sake bude makarantu

Ma’aikatar ilimi a jihar Zamfara ta sanar da sake bude makarantu a yau Litinin. Cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta sanar da cewa za a bude makarantun firamare da na sakandire a yau. Kazalika sanarwar ta ce makarantun gaba da sakandire kuma za su kasance a rufe har sai Continue reading
Labarai

‘Ya kamata shugaban kasa da gwamnoni su hana auren wuri’ -kungiyar kare hakkin dan Adam

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta ce auren wuri yana karuwa a kasarnan ne saboda gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi ba su dauki wata doka ta hana shi ba. A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce Najeriya ce kan gaba a nahiyar Afirka wajen aurar da yara mata da […]Continue reading
Labarai

Shugaba Buhari ya umarci sojojin Najeriya da su yi amfani da karfi wajen murkushe yan bindigar

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci sojojin kasarnan da su yi amfani da karfi wajen murkushe ’yan bindigar da ke kashe-kashe da garkuwa da mutane a Jihar Neja. Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya fitar a jiya ta ce shugaban kasar ya bayar da umarnin ne ga helkwatar Continue reading