Labarai

‘Ina kan matsaya ta cewa ba ni na kashe Haanifa ba’ – Abdulmalik Tanko

Mamallakin makaranta a Kano, Abdulmalik Tanko, da ake tuhuma a gaban kotu tare da wasu bisa zargin sacewa da kashe dalibarsa mai suna Hanifa Abubakar, a jiya ya fara kare kansa inda ya musanta aikata laifin. Abdulmalik Tanko mai shekaru 34 tare da Hashimu Isyaku dan shekara 37 da Fatima Musa Continue reading
Labarai

Na shiga tsakanin Dalladi Sankara Da Isa Gerawa saboda ne saboda sasanto

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya shiga tsakani tare da sasanta rikicin siyasar da ke tsakanin manyan mutane biyu a siyasar jihar Jigawa wato Sanata Danladi Abdullahi Sankara da Alhaji Isa Muhammed Gerawa. A karshe taron sulhun da aka gudanar a gidan Gwamnan dake Abuja ya kawo karshen Continue reading
Labarai

Hukumar bunkasa ilmin manya ta jihar Jigawa ta kaddamar da shirin rabon akwatinan radio karkashin shirin ta na koyarwa ta hanyar radio

Hukumar bunkasa ilmin manya ta jihar Jigawa ta kaddamar da shirin rabon akwatinan radio masu amfani da hasken rana da kayayyakin koyon karatu, karkashin shirin ta na koyarwa ta hanyar radio wanda gwamnatin jiha ta dauki nauyi. A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a cibiyar koyan karatun manya Continue reading
Labarai

‘Yan sanda a jihar Neja sun ce sun dakile harin da ‘yan bindiga suka kai kauyen Jellako da ke karamar hukumar Rafi a jihar

‘Yan sanda a jihar Neja sun ce sun dakile harin da ‘yan bindiga suka kai kauyen Jellako da ke karamar hukumar Rafi a jihar. Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Wasiu Abiodun, ya bayyana haka jiya a Minna, inda ya ce ‘yan bindiga da dama ne suka tsere da raunukan harbin bindiga, sannan aka sako Continue reading
Labarai

Hukumar ilimi matakin farko ta jihar Jigawa ta yi bikin bude bada tayin kwangilar gina azuzuwa 180

Hukumar ilimi matakin farko ta jihar Jigawa ta yi bikin bude bada tayin kwangilar gina azuzuwa 180 da kuma gyaran wadanda suka lalace 288 a wasu daga cikin makarantun jihar nan. A jawabinsa wajen bikin bude bayar da tayin kwangilar wakili a Hukumar, Alhaji Nuhu Muhammad wanda ya wakilci Continue reading
Labarai

Kungiyar dalibai ta kasa NANS ta baiwa gwamnatin tarayya da ASUU wa’adin kwanaki tara da su bude makarantu

Kungiyar dalibai ta kasa NANS reshen kudu maso gabas ta baiwa gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i ASUU wa’adin kwanaki tara na su bude dukkanin jami’o’in gwamnati. Ko’odinetan NANS shiyyar Kudu maso Gabas, Moses Onyia, ya bayar da wa’adin ne a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka Continue reading
Labarai

Mele Kyari ya bayar da tabbacin kawo karshen dogayen layukan man da ake yi a gidajen mai

Manajan Darakta na kamfanin man fetur ta kasa NNPC, Mele Kyari, ya bayar da tabbacin kawo karshen dogayen layukan man da ake yi a gidajen mai a kasar. Mele Kyari ya bayyana haka ne jiya a Abuja lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai kan halin da matatun man Continue reading
Labarai

Hukumar NDLEA ta kama akalla mutane 303 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a jihar Kaduna

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA reshen jihar Kaduna tace jami’anta sun kama akalla mutane 303 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a watannin ukun farkon 2022 a jihar Kaduna. Kwamandan NDLEA na jihar, Umar Adoro, shine ya sanar da haka ga kamfanin dillancin labarai na kasa Continue reading
Labarai

Majalisar wakilai ta kasa za ta gudanar da zama yau domin gyaran dokar zabe ta 2022

Majalisar wakilai ta kasa za ta gudanar da zama a gobe domin gyaran dokar zabe ta 2022. Magatakardar majalisar, Yahaya Danzaria, cikin wata sanarwa da ya fitar a yau yace ‘yan majalisar za su zauna domin gyaran wani babban kuskure a dokar. Tunda farko, majalisar dattawa ta gyara sashe na 84, Continue reading
Labarai

Rundunar ‘yansandan jihar Kebbi ta gabatar da cakin kudi na naira miliyan 60 ga iyalan jami’an ‘yansanda 6 da ‘yan fashin daji suka kashe

Rundunar ‘yansandan jihar Kebbi a yau ta gabatar da cakin kudi na naira miliyan 60 ga iyalan jami’an ‘yansanda 6 da ‘yan fashin daji suka kashe a bakin aiki. ‘Yansandan sun rasu yayin arangama da ‘yan fashin daji lokacin da suke aikin gadi a kamfanin kayan abinci na GB a kauyen Gafara dake Continue reading