Labarai

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero murnar karramawar da jamhuriyar Senegal ta yi masa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero murnar karramawar da jamhuriyar Senegal ta yi masa na “National Order of Lion”. Shugaba Macky Sall ne ya karrama sarkin a fadar shugaban kasa dake Dakar babban birnin kasar, bayan ziyarar da sarkin ya kai kasar kwanakin Continue reading
Labarai

Taliban ta umurci mata masu gabatar da shirye-shiryen talabijin na Afganistan da sauran matan da ke bayyana a talabijin da su rufe fuskokinsu yayin da ake haska su

Taliban ta umurci mata masu gabatar da shirye-shiryen talabijin na Afganistan da sauran matan da ke bayyana a talabijin da su rufe fuskokinsu yayin da ake haska su. Wani mai magana da yawun ‘yan Hisbah ya shaidawa manema labarai cewa an shaida wa kafafen yada labarai wannan dokar a ranar Continue reading
Labarai

Gwamna Nasir El-Rufa’i ya tabbatar da kasancewar ‘yan ta’addar Ansaru da sauran miyagun mutane a jihar Kaduna

Gwamna Nasir El Rufa’i na jihar Kaduna ya tabbatar da kasancewar ‘yan ta’addar Ansaru da sauran miyagun mutane a jihar. Nasir El-Rufa’i ya bayyana hakan ne a jiya a yayin taron majalisar tsaro na jihar inda ya saurari bayanai daga kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Continue reading
Labarai

Hukumar kula da tsaftar muhalli ta jihar Jigawa JISEPA ta kaddamar da aikin yashe magudanan ruwa a Dutse na tsawon makonni biyu

Hukumar kula da tsaftar muhalli ta jihar Jigawa JISEPA ta kaddamar da aikin yashe magudanan ruwa a Dutse na tsawon makonni biyu. Mukaddashin manajan daraktan hukumar, Injiniya Lawan Ahmed Zauma ne ya kaddamar da aikin a titin Hakimi street dake Dutse. Da yake jawabi yayin kaddamarwar, Ahmed Continue reading
Labarai

Gwamnatin Jihar Jigawa ta kammala sama da kashi 95 cikin 100 na ayyukan data gada daga gwamnatocin da suka gabata wadanda kudinsu ya haura naira miliyan dubu 96

Gwamnatin Jihar Jigawa ta kammala sama da kashi 95 cikin 100 na ayyukan data gada daga gwamnatocin da suka gabata wadanda kudinsu ya haura naira miliyan dubu 96. Darakta Janar na hukumar tantance ayyukan kwangila ta jihar Jigawa, Ado Hussaini, ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da Continue reading
Labarai

Rashin wadattacen abinci yana da nasaba da sare bishiyoyi bisa rashin ka’ida a Najeriya

Shugabar Hukumar Kula da Muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya, Rhoda Dia, ta ce kimanin kashi 97 cikin 100 na al’ummar Najeriya har yanzu suna amfani da itace wajen dafa abinci da sauran ayyuka. Rhoda Dia ta bayyana haka ne jiya a wajen wani taron tattaunawa na wuni biyu na masu ruwa da tsaki na Continue reading
Labarai

Hukumar EFCC ta samu umarnin kotu na tsare Akanta Janar na tarayya Ahmed Idris na karin wasu kwanaki

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta samu umarnin kotu na tsare Akanta Janar na tarayya Ahmed Idris na karin wasu kwanaki. Wani jami’in hukumar da bai so a ambaci sunan sa ba, ya bayyana cewa sashin shari’a na hukumar ne ya tabbatar da hakan cikin sa’o’i 24 Continue reading
Labarai

Hukumar tsaron fararen hula na Civil Defense ta tarwatsa wasu gungun barayin babura dake addabar mutanen karamar hukumar Jahun a jihar Jigawa

Hukumar tsaron fararen hula civil defense ta tarwatsa wasu gungun barayin babura dake addabar mutanen karamar hukumar Jahun a jihar Jigawa. Kakakin hukumar reshen jihar Jigawa, Adamu Shehu, ya tabbatar da haka ga manema labarai a Dutse, babban birnin jiha. Yace jami’an hukumar sun samu nasarar Continue reading
Labarai

Babban bankin kasa (CBN) ya yi kira ga manoman da suka ki biyan basussukan da aka basu a karkashin shirin Anchor Borrowers da su biya

Babban bankin kasa (CBN) ya yi kira ga manoman da suka ki biyan basussukan da aka basu a karkashin shirin Anchor Borrowers da su biya. Wani ma’aikaci a ofishin hada-hadar kudi na CBN, Sadeeq Ajayi, ya yi wannan roko a jiya a Ibadan, babban birnin jihar Oyo. Shirin Anchor Borrowers’ shiri ne na Continue reading
Labarai

Dakarun Operation Delta Safe da sun gano tare da lalata haramtattun matatun man fetur guda 167 a yankin Neja Delta cikin makonni 3

Helkwatar tsaro tace dakarun Operation Delta Safe da na Operation Dakatar da Barawo, sun gano tare da lalata haramtattun matatun man fetur guda 167 a yankin Neja Delta cikin makonni 3. Daraktan yada labaran tsaro, Manjo Janar Bernard Onyeuko, shine ya sanar da haka a yau yayin da yake jawabi ga Continue reading