0 123

Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam sun shiga ruɗani kan makomar ‘yan cirani a Libya

Ƙungiyoyin kare hakkin bil adama sun shiga cikin ruɗani da fargabar makomar masu neman mafaka, yayin da Amurka ta bayyana shirin tasa ƙeyar dubban baƙin haure zuwa Libya.

Gwamnatin Trump na ci gaba da faɗaɗa ƙoƙarinta na kawar da baƙin haure zuwa wasu ƙasashe uku, duk da kalubalen shari’a da take fuskanta.

A ranar Laraba ne wata kotu a Amurka, ta yanke hukuncin cewa ba za a iya korar baƙin hauren ba tare da ba su damar kalubalantar matakin da aka ɗauka a kansu a gaban kotu ba.

Ko da yake, gwamnatocin Libya da ke hamayya da juna, sun ce ba za su amince da karɓar mutanen da aka kora  musu ba, sannan kuma tsarin da kasar ke da shi na tauye hakkin masu neman mafaka, ya ɗiga ayar tambaya kan makomar baƙin hauren.

Libya babbar cibiyar zirga-zirga ce ga masu neman mafaka da ke ƙoƙarin isa Turai kuma a kowace shekara, dubban mutane ne ke yunƙurin tsallakawa zuwa tekun Bahar Rum.

Kimanin baƙin haure 800,000 ne a halin yanzu kezaune a kasar Libya inda rahotanni ke ci gaba da bayyana yadda ake musguna musu.

Tawagar bincike mai zaman kanta ta Majalisar Ɗinkin Duniya, a shekara ta 2024 ta gano shaidar da ke nuna cewa an aikata laifukan cin zarafin bil adama a kan baƙin hauren da ke Libya.

Rahoton binciken ya kuma gano gawawwakin baƙin haure a cikin manyan ƙaburbura a sassan kasar, yayin da dubun dubatar wasu suka nutse a ruwa a lokacin da suke ƙoƙarin tserewa daga ƙasar.

Leave a Reply