Shugaban karamar hukumar Hadejia, Alhaji Ahmed Abba Ari, ya bayyana haka yayin ƙaddamar da shirin allurar a kauyen Fulani na Mushimbura. Ya ce wannan mataki na daga cikin manufofi 12 na gwamnati karkashin jagorancin Gwamna Malam Umar Namadi, wanda ke mayar da hankali kan kiwon lafiya da tsaftar dabbobi.
Ya yi kira ga makiyaya da su fito da dabbobinsu zuwa cibiyoyin da aka tanada domin su amfana da wannan shirin, wanda gwamnatin jihar ta dauki nauyinsa ta hannun ma’aikatar noma – kuma ana yin shi kyauta ba tare da biyan kuɗi ba.
Shugaban sashen aikin gona na karamar hukumar, Alhaji Suleiman Makama Auyo, ya bayyana cewa an tanadi cibiyoyi guda biyar a fadin karamar hukumar domin sauƙaƙa gudanar da aikin. Ya kara da cewa an ɗauki ma’aikata ad-hoc guda ashirin da ɗaya da aka horar, domin gudanar da shirin cikin tsari. Haka kuma, ana ci gaba da yi wa dabbobi rigakafi a kullum a cibiyoyin dabbobi da ke yankin.
A nasa jawabin na godiya a madadin makiyaya, wakilin ƙungiyar Kautal Hore, Malam Isale, ya yaba wa haɗin gwiwar gwamnatin jiha da ta karamar hukuma wajen kawo musu irin wannan tallafi mai muhimmanci.