Aƙalla mutane uku ne suka rasu a wani sabon rikicin manoma da makiyaya a Jihar Nasarawa

0 129

Aƙalla mutane uku ne suka rasu a wani sabon rikicin manoma da makiyaya a yankin Dogon Duste da ke tsakanin ƙananan hukumomin Nasarawa da Toto a Jihar Nasarawa.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Umar Nadada ne tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Litinin 18 ga watan Nuwamba da misalin ƙarfe 4:30 na yamma.

Jami’in ’yan sandan shiyyar ya ruwaito cewa, da isar su wurin, suka gano gawarwakin mutum biyu a gonar, wasu hudu kuma sun jikkata, nan take kuma aka kai waɗanda suka jikkata zuwa cibiyar kula da lafiya a matakin farko domin yi musu magani.

A wani bincike da ’yan sandan suka gudanar, sun gano wata gawa a cikin daji, wanda ya kawo adadin waɗanda suka mutu zuwa uku. Kwamishinan ya tabbatar da cewa an daidaita al’amura a yankin, kuma jaddada mahimmancin haɗin kan al’umma wajen tabbatar da tsaro, sannan ya buƙaci mazauna yankin da su ba jami’an tsaro haɗin kai domin hana afkuwar irin haka a nan gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: