Aƙalla mutum 5 ne suka rasa rayukansu a yayin wata fashewa da ta auku a birnin Mogadishu

0 223

Wata fashewa da auku a wurin shan shayi da ke tsakiyar birnin Mogadishu ta kashe aƙalla mutum biyar yayin da suke tsaka da kallon wasan ƙarshe na gasar ƙwallon ƙafa ta ƙasashen Turai.

Haka nan, bam ɗin da aka ɗana a jikin mota ya jikkata aƙalla mutum 20, in ji rundunar ‘yansandan Somalia, yayin kallon wasan da Sifaniya da doke Ingila 2-1 kuma ta ɗauki kofin gasar ta Euro 2024 a daren jiya Lahadi.

Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook, rundunar ta ce motar da aka ajiye a kusa da shagon mai suna Top cafe ce ta tarwatse.

Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 10:28 na dare, a cewar ‘yansandan.

Ɗaya daga cikin mutanen da suka tsira daga harin ya faɗa wa wata kafar yaɗa labaran yankin cewa yana cikin shagon da ake kallon wasan lokacin da bam ɗin ya tashi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: