A cewar Sakataren Harkokin Wajen Amurka ‘kasar Ukraine za ta yi gagarumar nasara a yaƙin da suke da Rasha’

0 163

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya shaida wa BBC cewa yana da yaƙinin Ukraine za ta yi nasara a yakin da suke yi da Rasha.

Mista Blinken ya ce ba zai fadi yadda hakan ko tsahon lokacin da za a ɗauka ana yakin tsakanin kasashen biyu ba, sai dai ya yi watsi da batun Rasha ka iya cimma burinta a kan mutum miliyan 45 da ke yakin kwatar ‘yancinsu.

Blinken ya bayyana haka ne a Brussels a kan hanyarsa ta zuwa kasar Poland.

Wakiliyar BBC ta ce ana sa ran da zarar sakataren harkokin wajen ya isa Poland zai kai wa ‘yan gudun hijirar Ukraine ziyara da kara jaddada goyon baya ga kasar.

Sai dai firaministan Poland ya ce yana fargabar kar Rasha ta kai hari wajen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: