A karon farko jam’iyyar ANC na dab da rasa rinjaye a majalisar dokokin a ƙasar Afirka ta Kudu

0 170

Sakamakon wani ɓangare na zaben ƴan majalisar dokokin ƙasar Afirka ta Kudu ya nuna cewa jam’iyyar ANC mai mulkin ƙasar tun a shekaru 30 da suka gabata, na dab da rasa rinjaye a majalisar dokokin kasar a karon farko.

Yayin da aka ƙidaya kashi 56 cikin 100 na gundumomin zabe, jam’iyyar ANC ce ke kan gaba da kashi 42 cikin 100, sai kuma Democratic Alliance (DA) da kashi 24 cikin 100.

Jam’iyyar MK ta tsohon shugaban kasar Jacob Zuma ta samu kashi 11 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, yayin da jam’iyyar Economic Freedom Fighters ke mara baya da kusan kaso 10.

Ana sa ran sakamakon ƙarshe na zaɓen a karshen wannan mako.

Sai dai na’urar da ke nuna sakamakon zaben kai tsaye ta samu cikas da safiyar Juma’a, inda ta nuna babu sakamako.

Hukumar zaɓen dai ta nemi afuwar cikas ɗin da aka samu, daga bisani kuma na’urar ta dawo aiki, tare da tabbatar wa jama’a cewa sahihancin sakamakon zaben yana nan daram.

Leave a Reply

%d bloggers like this: