A karon farko yawan wutar lantarki ya karu zuwa megawatt dubu 5,313

0 72

Yawan wutar lantarki ya karu zuwa megawatt dubu 5,313 a ranar Litinin da ta gabata, karo na farko cikin shekaru uku, a cewar Ma’aikatar Wutar Lantarki.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Bolaji Tunji, Mai ba da shawara ta musamman kan Harkokin Sadarwa da Hulda da Jama’a ga Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya fitar.

Adelabu ya bukaci Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki, DisCos, da su yi amfani da ƙarin wutar domin kaucewa katsewar layikan wutar lantarkin.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa a watan Mayu, gwamnatin tarayya ta yi alkawarin samar da megawatt 6,000 na wutar lantarki kafin karshen shekarar nan.

Yayin gabatar da jawabin sa a babban birnin tarayya Abuja, lokacin da yake bayyana nasarorin ma’aikatarsa tun bayan da Shugaban kasa Bola Tinubu ya kama aiki a ranar 29 ga Mayu, 2023, Adelabu ya ce yawan wutar lantarki na kasa ya kai megawatt 5,000 a ranar 3 ga Mayun da ya gabata.

Adelabu ya kuma jaddada alkawarin cewa yawan wutar lantarkin zai kai megawatt 6,000 kafin karshen wannan shekara, duba da ci gaban da aka samu a fannin makamashi a shekarar 2023.

Leave a Reply

%d bloggers like this: