A shirye muke mu gana da Shugaba Tinubu kan bukatar rage farashin man fetur – NANS

0 86

Shugaban Kungiyar Dalibai ta Kasa (NANS) ya ce a shirye  suke su gana da shugaban kasa Bola Tinubu idan akwai bukata, kan bukatar ta na ganin an rage karin farashin man fetur din da akayi.

Sakataren kungiyar dalibai ta kasa (NANS), David Bariereka ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels a garin Fatakwal na jihar Ribas.

A cewarsa, a halin yanzu kungiyar daliban na tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar man fetur da suka hada da dan kasuwa Aliko Dangote, da ‘yan kasuwar man fetur, da karamin ministan man fetur, domin lalubo hanyar magance matsalolin da jama’a ke fuskanta.

Wannan ci gaban na zuwa ne bayan kungiyar daliban ta dage kan ci gaba da gudanar da zanga-zangar adawa da karin farashin man fetur a fadin kasar.

Tun da farko kungiyar ta sanya ranar 15 ga Satumba, 2024, don yajin aikin na kasa baki daya. Ya jaddada cewa shugabancin Kungiyar yana da aniyar warware dukkan hanyoyin tattaunawa da kuma tuntubar hukumomin da abin ya shafa kafin su fara zanga-zanga.

Leave a Reply

%d bloggers like this: