A zangon farko na 2025 an bankado matsalar raguwar kashe kuɗaɗe a muhimman sassan ruwa da lafiya – JIGAWA
Rahoton aiwatar da kasafin kuɗin jihar Jigawa a zangon farko na shekarar 2025 ya bankado matsalar gagarumin raguwar kashe kuɗaɗe a muhimman sassan ruwa da lafiya.
Rahoton ya nuna cewa daga cikin naira biliyan 11.7 da aka ware wa Ma’aikatar Ruwa, an kashe kashi 5.4% kacal, yayin da Hukumar Samar da Ruwa da Tsabtace Muhalli a karkara ba ta samu ko sisi ba, duk da cewa an ware mata sama da naira biliyan 3.6.
Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da alkaluman Hukumar Kididdiga ta Ƙasa ke nuna cewa kashi 12 cikin 100 na iyalai a jihar na fama da karancin ruwan sha mai tsafta.
A bangaren lafiya ma, ana fuskantar matsala, inda aka kashe kashi 8.3% kacal daga cikin naira biliyan 42.5 da aka ware wa manyan ayyukan lafiya, lamarin da ke haifar da tambayoyi kan yadda gwamnati ke aiwatar da ayyukan jin ƙai.