Abin Mamaki: Gwamnan Kaduna Ya Sa Ɗansa A Firamaren Gwamnati

0 316

A ranar Litinin ne Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya sa ɗansa mai shekaru shida da haihuwa, Abubakar Al-Siddique El-Rufa’i a makarantar firamare mallakin Gwamnatin Jihar, Kaduna Capital School.

Ana ganin hakan a matsayin wani cika alƙawarin kamfe da Gwamna El-Rufa’i ya yi a 2017, lokacin da ya bayyana yunƙurinsa na gyara ɓangaren ilimi a jihar.

Da yake rubutu a shafinsa na Twitter a ranar 28 ga Disamba, 2017, Malam Nasir @elrufai ya ce: “Ta hanyar buga misali, zan tabbatar da cewa ɗana wanda zai cika shekaru shida da haihuwa a 2019 ya shiga makarantar gwamnati a Jihar Kaduna idan Allah Ya yarda.

“A yau Abubakar Al-Siddique El-Rufa’i ya zama ɗalibin Aji Ɗaya na Firamare na Kaduna Capital School.

Leave a Reply

%d bloggers like this: