Abubuwan da ya kamata ku sani game da Yau Ranar Ƴancin Ƴan jarida Ta Duniya

0 266

Ranar ‘yancin ‘yan jarida wato 3 ga watan Mayun kowace shekara, rana ce da majalisar dinkin duniya ta kebe domin fadakar da jama’a game da illolin hana kafafen yada labarai tsage gaskiya komai dacinta.

Bayanai na nuna cewa, ‘yan jarida a sassa daban-daban na duniya suna fuskantar barazana, har a wasu lokuta ta kai ga an daure su a gidan kaso ko rasa rayukansu yayin da suke gudanar da ayyukansu.

Wannan ya sa ‘yan jarida ba sa samun damar sauke nauyin da ke wuyansu na sanar da al’umma irin abubuwan da ke faruwa a sassa daban-daban na duniya, musamman abubuwan da gwamnatoci ko shugabanni suke gudanarwa a kasashensu.

Masu sharhi na bayyana cewa, duk da kokarin da kungiyoyin ‘yan jaridu ke yi, na fadakar da jama’a game da muhimmancin aikin har yanzu, ana fuskantar rashin jituwa tsakanin ‘yan jarida da wasu gwamnatocin kasashe..

Sai dai wasu na alakanta hakan da yadda wasu ‘yan jaridan ke kaucewa dokoki da ka’idojin aikin, maimakon haka suke karkata ga cin zarafin jama’a ko jirkita rahotannin domin biyan bukatun wasu, wadanda a mafi yawan lokuta kan kai ga tashe-tashen hankula har ma da zubar jini.

Leave a Reply

%d bloggers like this: