ACReSAL ta ƙasa ta nuna jin daɗi kan yadda shirin Jigawa ACReSAL ke gudanar da ayyukan raya noma

0 129

Shirin ACReSAL na ƙasa ya nuna gamsuwa da jin daɗi kan yadda shirin Jigawa ACReSAL ke gudanar da ayyukan raya noma, walwalar jama’a, yaki da ambaliya da inganta ruwa.

Shugabar tawagar duba aikin daga matakin ƙasa, Dr Joy Aganne, ta bayyana haka yayin rufe aikin duba ci gaba na shekarar 2025 da aka gudanar a Abuja, tana mai jinjina wa jihar Jigawa bisa irin kyakkyawan jagoranci.

Dr Aganne ta yi alkawarin haɗin gwiwa da cikakken goyon bayan Bankin Duniya da shirin na ƙasa domin ganin ana ci gaba da samun nasarori masu ɗorewa.

A nasa jawabin, ko’odineta na Jigawa ACReSAL, Alhaji Yahaya Muhammad Ubah Kafingana, ya yaba da hadin kai daga gwamnatin Jigawa da sauran abokan hulɗa, yana mai cewa za su ƙara himma don ci gaban al’ummarsu.

Leave a Reply