Adadin ƴan Najeriya da ke fama da talauci zai iya zarce hasashen Bankin Duniya

0 92

Masana tattalin arziƙi sun yi gargaɗin cewa adadin ƴan Najeriya da ke fama da talauci na iya zarce hasashen Bankin Duniya na mutane miliyan 104, sakamakon hauhawar farashin fetur da matsalolin samar da abinci da ƙasar ke fuskanta.

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan masu fama da talauci a Najeriya ya ƙaru zuwa kashi 46 cikin 100 a shekarar 2023, wanda ke nuni da mutane miliyan 104 ne  ke fama da ƙangin talauci a ƙasar.

A cikin rahoton da bankin ya fitar an nuna yadda adadin masu fama da talauci ya tashi daga kashi 40 cikin 100 a shekarar 2018 zuwa kashi 46 cikin 100 a shekarar 2023, yayin da adadin talakawa ya ƙaru daga miliyan 79 zuwa miliyan 104.

Rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki da ƙarancin ci gaban tattalin arziki ya jefa karin mutane miliyan 24 cikin talauci, inda adadin talakawa a birane ya ƙaru daga miliyan 13 zuwa miliyan 20, yayin da a karkara ya ƙaru daga miliyan 67 zuwa miliyan 84.

Duk da cewa Bankin Duniyar ya yi hasashen cewa sauye-sauyen tattalin arziƙin Shugaban kasa Bola Tinubu daga shekarar 2024 zuwa 2026 za su rage ƙaruwar talauci, wasu masana sun bayyana cewa ƙarin farashin man fetur da wasu manufofi na gwamnati za su sa yawan talakawan ya zarce wannan hasashe saboda tsadar kayayyaki da rashin ƙaruwar albashi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: