Adadin ma’aunin arzikin cikin gida (GDP) na jihar Jigawa ya karu daga naira miliyan 950,000 zuwa sama da naira tiriliyan 2 a sakamakon fadada ayyukan noma

0 90

Adadin ma’aunin arzikin cikin gida (GDP) na jihar Jigawa ya karu daga naira miliyan dubu 950 zuwa sama da naira tiriliyan biyu a sakamakon fadada ayyukan noma da gwamnatin jihar ta yi.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin tawaga daga cibiyar bincike ta tafkin Chadi a gidan gwamnati dake Dutse babban birnin jihar.

Gwamna Badaru Abubakar ya shaidawa tawagar cewa jihar Jigawa ta himmatu wajen bunkasa harkar noma domin inganta samar da abinci da tattalin arzikin al’umma.

Ya kuma yi alkawarin ci gaba da hada kai da cibiyar bincike ta tafkin Chadi wajen inganta binciken iri da sauran ayyukan noma.

Tun da farko, a nasa jawabin daraktan bincike na cibiyar, Dr Zakari Turaki, ya ce cibiyar binciken ta tafkin Chadi tare da hadin gwiwar cibiyar bincike ta jihar Jigawa ta bullo da wani sabon nau’in irin alkama mai suna Maja wanda hukumar tabbatar da iri ta kasa dake Ibadan ta amince da shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: