Adadin mutuwar mata masu juna biyu yana ƙara yawaita a jihar Kano

0 64

Kakakin majalisar dokokin jihar kano Hamisu Ibrahim ya bayyana damuwarsa dangane da yawaitar mata masu juna biyu da ke rasa rayuwarsu a lokacin haihuwa a duka sassan jihar.

Kakakin ya kuma ce majalisar tana shirin kaddamar da shirin duba lafiyar masu juna biyu da kananan yara kyawta.

Hamisu Ibrahim ya bayyana hakan a wajen zaman kwamatin majalisar mai yaki da illar da kuma manyan masu ruwa da tsaki a majalisar wanda ya gudana a jihar kaduna. Kazalika kakakin yabada tabbacin aiki tukuru domin ganin an nemo bakin zaren matsalar tare da fatan samun kyakkyawan sakamako.

Leave a Reply

%d bloggers like this: