Ado Doguwa Ya Lashe Zaɓen Kujerar Wakilcin Doguwa Da T/Wada

0 292

A wani labarin makamancin wannna, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta bayyana shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai Alhassan Doguwa a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar tarayya ta Tudunwada/Doguwa a jihar Kano.
Alhassan Doguwa ne ya yi nasara a karashen zaben da aka gudanar jiya a yankin.
Jami’in zabe na hukumar INEC, Farfesa Sani Ibrahim ne ya sanar da sakamakon, inda ya ce dan takarar jam’iyyar APC ya samu kuri’u dubu 41 da 573.
Babban abokin hamayyarsa kuma dan takarar jam’iyyar NNPP, Yushau Salisu, ya samu kuri’u dubu 34 da 831, yayin dan takarar jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 211.
A wani labarin kuma, Dan takarar jam’iyyar NNPP, Mohammed Bello Shehu ya lashe zaben majalisar wakilai ta tarayya Fagge a jihar Kano.
Bello Shehu ya doke dan majalisar wakilai mai ci, Aminu Sulaiman Goro na jam’iyyar APC inda ya kawo karshen wakilcinsa na shekaru 12 a majalisar.

Leave a Reply