Aiki karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba ni damar kwarewar tafiyar da Najeriya – Farfesa Osinbajo

0 76

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a jiya ya ce aiki karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba shi damar kwarewar tafiyar da Najeriya.

Yemi Osinbajo ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci Alake na Egbaland a fadarsa da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Ziyarar dai wani bangare ne na tuntubar wasu fitattun mutane da wakilan jam’iyyar APC da mataimakin shugaban kasar ke yi domin neman goyon bayansu ga aniyarsa ta tsayawa takara a zaben 2023.

A jiya ne ya isa jihar Ogun inda ya gana da Gwamna Dapo Abiodun kuma gwamnan ya bayyana goyon bayan sa gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar a wata mai zuwa.

Yemi Osinbajo ya ce duk da cewa shi ba dan siyasa ba ne lokacin da jam’iyyar ta tsayar da shi a matsayin abokin takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2015; yanzu ya tsunduma cikin siyasa kuma zai iya jagorantar Najeriya.

Osinbajo ya ce yana da kwarin gwiwar gudanar da ayyukansa a matsayinsa na shugaban kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: