Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya shigar da yara dubu 3, yawancinsu yayan talakawa, a manyan makarantu na musamman guda 2 dake kananan hukumomin Maiduguri da Jere.

Gwamnatinsa ce ta gina makarantun a yankunan kananan hukumomin Maiduguri da Jere dake da yaran dayawa da basa zuwa makaranta. An shirya makarantun da nufin kula da karatunsu.

Wata sanarwa da kakakin gwamnan, Mallam Isa Gusau, ya fitar, tace gwamna Zulum ya sanar a ranar Litinin yayin bude makarantun cewa gwamnati zata mika su ga al’umma domin su gudanar da su, yayin da gwamnatin zata biya albashin malamai.

A wani cigaban kuma, gwamnan ya kaddamar da sabon titin da magudanan ruwa a unguwar Maromaro dake Maiduguri.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: