Mai bai wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Ajuri Ngelale, ya tafi hutun sai baba ta gani saboda rashin lafiya ba tare da shiri ba.
Ngelale ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne bayan shawarwari da iyalinsa suka ba shi, saboda wani mummunan yanayi na rashin lafiya da ya ƙara ta’azzara masa.
Ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya aikewa Shugaban Ma’aikatan Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, a yau Asabar.
Ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bayan tuntuɓar iyalinsa saboda yanayin rashin lafiyar da ke ƙara tsananta, kuma hakan ya sa dole ya dakatar da aikinsa na Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yada Labarai da sauran mukamansa.
Ngelale ya ƙara da cewa yana fatan dawowa bakin aikinsa idan ya samu sauki, idan kuma yanayi ya bayar da dama, sannan ya roki a bar shi, shi da iyalinsa na tsawon wannan lokacin.
Wannan hutun yana nufin zai dakatar da aikinsa na mai magana da yawun Shugaban kasa Bola Tinubu na tsawon lokacin da zai ɗebe yana jinyar.